Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga ‘yan kasar mazauna Ukraine su gaggauta tattara ya-na-su-ya-na-su kuma su fice daga kasar ba tare da ɓata lokaci ba.
A wata hira da gidan talbijin na NBC, Mista Biden ya ce: “Amurkawa su fice daga Ukraine nan take, lamurra za su iya dagulewa cikin sauri, domin sojojin Amurkar ba za su samu damar zuwa kwashe su ba.”
Rasha ta sha musanta cewa tana shirin afka wa Ukraine duk da cewa ta jibge dakaru 100,000 a kusa da iyakarta.
Sai dai ta fara wani atisayen soja tare da maƙociyarta Belarus, sannan Ukraine ta zargi Rashar da rufe mata hanyar kaiwa ga teku.
Fadar Kremlin ta Rasha ta ce tana so ta “shata layi” don tabbatar da cewa tsohuwar mambanta a tsohuwar Tarayyar Soviet ba ta shiga ƙungiyar tsaro ta Nato.