News
Nan da watanni 10 za mu kammala kasuwar gwala-gwalai ta Kano — Gwamnatin Taraiya
Daga yasir sani abdullahi
Gwamnatin Taraiya ta yi alƙawarin kammala kasuwar gwala-gwalai, wacce a ka fara ginawa a Jihar Kano, nan da watanni 10.
Ministan Cigaban Ma’adanai da Ƙarafa, Olamilekan Adegbite ne ya baiyana haka bayan da ya kai ziyarar gani-da-ido, kamar yadda ke ƙunshe a wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Idowu Jokpeyibo ya fitar.
Sanarwar ta ce gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin kammala kasuwar gwala-gwalai da a ke ginawa a Kano nan da ƙarshen 2022.
“Samar da kasuwar gwala-gwalai ta Kano wani yunƙuri ne na gwamnatin nan na samar da ƙananan masana’antun ma’adanai a shiyyoyi shida na ƙasar nan domin samar da bunƙasar sana’ar ma’adanai a ƙasar nan.
“Kasuwar gwala-gwalan, wacce a ke gina ta Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar, idan a ka kammala ta, to za ta kara da kasuwannin gwala-gwalai na duniya, in ji ministan.
“A cewar ministan, amfanin yin kasuwar shi ke zai ƙara wasu hanyoyin na tattalin arziki. “Mu na son gwal ɗin mu ya haɓɓaka a nan. Za mu haɓɓaka tattalin arziki. Za a ɗauki ma’aikata kuma za a Tarawa gwamnati kuɗaɗen shiga.
“Ya na da muhimmaci mu ƙara inganta gwal ɗin mu, a maimakon mu riƙa fita da tsuran shi ƙasashen waje. Za mu yi sarƙoƙi, awarwaro, agoguna, ɗan kunnaye da sauran su. Da haka ne mutane za su ji cewa akwai kasuwar gwala-gwalai a Nijeriya kuma za su zo su siya kamar yadda su ke saya a ƙasashen waje,” in ji sanarwar.