News
Zamfarawa sun yi ƙorafi kan yadda Gwamna Matawalle ke tsallen-gada bisa rahoton kwamitin da ya bankaɗo masu laifi a kashe-kashen jihar.
Daga yasir sani abdullahi
Gwamna Matawalle ya bai wa Majalisar Dokoki da Kotunan Zamfara ‘yancin gashin kan su
Al’ummar Jihar Zamfara na ci gaba da nuna damuwar su kan yadda Gwamna Bello Matawalle ya ƙi yin amfani da shawarwarin Da Rahoton Kwamitin Musabbabin Rikicin Zamfara Da Yadda Za A Magance Shi a jihar.
Kwamitin dai a cikin 2019 ne Gwamna Matawalle ya kafa shi da kan sa, wanda aka ɗora tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar a matsayin Shugaban Kwamiti. Kwamitin ya miƙa wa gwannan rahoton abin da ya bankaɗo, kuma ya lissafa waɗanda ke da hannu, yawan asarar da aka yi, waɗanda aka kashe da waɗanda aka raba da gidajen su. Hatta yawan marayu da zawarawa mata da masu takabar da aka mutu aka bari, duk kwamitin ya lissafa.
Kuma ya lissafa waɗanda za a hukunta, saboda samun su da haɗa baki da ‘yan bindiga. Tun cikin Oktoba 2019 kwamitin ya miƙa wa gwannan rahoton sa.
Yayin da Gwamna ke cewa ya yi aiki da wasu shawarwari da kwamitin ya bayar, al’ummar Zamfara na cikin halin nuna rashin yarda da hakan. Su na zargin gwamnan ya na tuma tsallen gada kan rahoton, ya na tattake shi.
PREMIUM TIMES a cikin 2019 ta buga labarin kwamitin ya ce ya yi nazarin lamarin ‘yan bindiga a Jihar Zamfara, tun daga Yuni 2011 zuwa Mayu 29 na shekarar 2019, ranar da Matawalle ya kama mulki.
Daga 2011 zuwa 2019 ɗin kuwa, duk lokacin tsohon Gwamna Abdul’aziz Yaro ne da Matawalle ya gada.
Matawalle ya kafa kwamitin a lokacin da ya ke cikin jam’iyyar PDP. Sai dai kuma a yanzu ya na cikin jam’iyya mai mulki, wato APC.
A lokacin da aka damƙa masa rahoton, Abubakar Shugaban Kwamiti ya ce tsakanin 2011 zuwa Mayu 2019 matan aure 4,983 sun rasa mazajen su, waɗanda ‘yan bindiga suka kashe.
Kwamitin ya ce a wadancan shekaru an samu yaran da aka maida marayu su 25,050. Sannan kuma an raba mutum 190,340 daga gidajen su.
Rahoto ya ci gaba da nuna cewa Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba sun rasa shanu 2,015, tumaki 141, jakai da raƙuma 2,600 sai kuma an yi asarar motoci da babura da sauran ƙananan ababen hawa 147,800 waɗanda aka banka wa wuta a yankuna daban-daban na jihar Zamfara.
Kwamiti ya ci gaba da cewa an yi asarar naira biliyan 3 waɗanda aka riƙa biyan ‘yan bindiga a matsayin kuɗin fansar waɗanda su ke yin garkuwa da su. An kuma yi garkuwa da mutum 3,672 a shekarun.
Haka kuma kwamitin ya kama sarakuna 5 da laifi, hakimai 33 da dagatai. An kuma samu wasu sojoji 10 da ‘yan sanda sun haɗa baki da ‘yan bindiga.
Yayin da ya ke karɓar rahoton, Matawalle ya yi alƙawarin zai yi amfani da shawarwarin da ke cikin sa, ba tare da wani abu ya ɗauke masa hankali daga aikata hakan ba.
Yayin da su ke tattauna batun a shafin ta na Tiwita, fitacciyar ‘yar jaridar nan wadda kuma ‘yar asalin Zamfara ce, Kadria Ahmed ta yi kira ga Gwamna Matawalle ya yi aiki da rahoton.
Ta ce rashin yin aiki da shawarwarin da kwamitin ya bayar koma-baya ne ga tsaron jihar Zamfara.
Shi kuwa Yahuza Getso, wani mai nazarin harkokin tsaro da tashe-tashen hankula, cewa ya yi shi kan sa kwamitin ma duk bige ce kawai.
“Abin da aka saki har jama’a suka sani a rahoton ai cikin cokali ne. Mun sha tambayar Gwamna ya ba mu rahoton ko kuma ya sa a buga shi a jaridu domin mu bi shi a tsakane, amms sun ƙi ba mu.
“Ni na san dama ba za a fitar mana da sakamakon binciken da kwamitin ya yi ba. Saboda akwai hukuncin da gwamnati ba ta iya ɗauka. Ko kuma akwai abin da ba ta so mu sani.”
Ita ma wata ƙungiya mai suna Zamfara Circle Initiative ts yi kira ga gwamnatin Zamfara ta yi aiki da rahoton kwamitin. Haka shugaban ƙungiyar mai suna Al-Amin Tsafe ya shaida wa wakilin mu.
Ya ce ƙin yin aiki da rahoton babbar illa ce ga tsaron jihar Zamfara.
Shi ma wani babban malamin jami’a a Jami’ar Usmanu Danfodiyo mai suna Tijjani Shinkafi, wanda ɗan jihar Zamfara ne, ya ce idan aka yi amfani da rahoton kwamitin, to hakan zai faranta rayukan al’ummar yankunan da bala’in ya fi shafa.
Daraktan Yaɗa Labarai na Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai na Zamani, na Gwamna Matawalle mai sun Ibrahim Zauma, ya ce masu sukar Gwamna kan wannan lamari ba su yi masa adalci ba.
Yayin da ya ce Matawalle ya fara aiki da wasu shawarwarin da kwamitin ya bayar, ya ce wasu shawarwarin kuwa Gwamnatin Tarayya ce kaɗai za ta iya aiwatar da su.