News
Rikicin APC a Kano: Babu sulhu idan har ba a bamu kashi 55 na muƙamai gami da shugabancin jam’iyya ba — Ɓangaren Shekarau
Daga kabiru basiru fulatan
Yayin da a ke ci gaba da gabza rikici a cikin jam’iya mai mulki APC a Jihar Kano, ɓangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ya ke jagoranta ya tsaya kai-da-fata cewa ba zai yarda da duk wani mataki na sulhun da a ke ƙoƙarin yi ba har sai an bashi kashi 55 na muƙaman jam’iya, da kuma muƙamin shugaban jam’iyya na jiha.
Ɓangaren na Shekarau, a wata wasiƙa da ya aikewa uwar jam’iya ta ƙasa a ranar 8 ga watan Fabrairu, ya ce ya yi fatali da duk wani ƙuduri na sulhu da shelkwatar jam’iyar ta ɗauka.
Haka-zalika, a wata wasiƙar ta ranar 9 ga Febrairu, wacce su ka sake aikewa shelkwatar jam’iya ta ƙasa, ɓangaren na Shekarau sun kafe a kan sai dai a basu kashi 55 na mukaman jam’iya gami da muƙamin shugaban jam’iya na jiha.
Waɗanda su ka sa hannu a sanarwar sun haɗa da Sanata Ibrahim Shekarau (APC-Kano Central), Sanata Barau Jibrin (APC-Kano North), Tijjani Jobe (APC- mazaɓar D/Tofa/Rimingado ), Nasiru Gabasawa (APC- mazaɓar Gezawa/Gabasawa ), Haruna Dederi (APC- mazaɓar Karaye/Rogo ), Sha’aban Sharada (APC- mazaɓar Kano Municipal ) da kuma Shehu Dalhatu (Shugaban Buhari Support Group).
Sun kuma nemi bangaren gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya janye ɗaukaka ƙarar da ya shigar a kan tsagin na Shekarau domin ƙalubalantar nasarar da su ka samu a Babbar Kotu a Abuja, wacce ta amince da zaɓen shugabannin jam’iya na jiha da su ka yi.
Sun ce in dai su na son su yadda da gaskiya bangaren na Ganduje, to sai dai su janye ɗaukaka ƙarar da su ka shigar.
Tsagin na Tsohon Gwamna Shekarau ya kuma nemi cewa ba zai sake yarda da matakin sulhu ba har sai an cire Ganduje da ga zama shugaban kwamitin sulhu a jihar Kano saboda da ɓangaren shi a ke yin rigimar.