News
Yanzu-Yanzu: ‘Yan sanda sun ba da shawarar rage girman Abba Kyari
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kwamitin ladabtarwa na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya ba da shawarar tsige kwamandan IRT da aka dakatar, DCP Abba Kyari, zuwa mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda.
Hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin bincike na musamman da ya binciki Kyari kan tuhumar da wata takardar shaidar da hukumar binciken ta Amurka ta yi.
Kwamitin ya gano cewa Kyari yana da alaka da ‘yan damfara sannan kuma ya saba wa tsarin kafafen sada zumunta na rundunar ‘yan sandan Najeriya ta hanyar mayar da martani kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta yi a shafinsa na Facebook ba tare da bin ka’ida ba.