Ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a birnin Petropolis na Brazil sun halaka kusan mutaum 100, inda yawancin mutane kuma suka rasa muhallansu.
Guguwar da aka yi da ruwan saman da aka sheka kamar-da-bakin-kwarya cikin awowi ƙalilan sun sa taɓo ya binne gidaje.
Matan Henrique na daga cikin wadanda suka tsira. Ya ce: “Yawancin mutane sun rasa duk abin da suka mallaka, ba su da komai, babu wurin kwanciya, babu abinci, komai kankantar abu zai faranta musu rai. wasu na bukatar wanda zai rungume su cikin tausayawa da ba da kwarin gwiwa.”
Tuni jihohi makota suka fara aika kayan agaji da injinan da za su taimaka a kwashe taɓo da bishiyoyin da suka kakkarye tare da rufe hanyoyi.
Tun da fari, a jiya Laraba Magajin Garin Petropolis ya ayyana dokar ta-baci a birnin.