Mutum aƙalla takwas ne ‘yan bindiga suka kashe a kasuwar shanu ta Jihar Abiya da ke kudu maso kudancin Najeriya ranar Talata, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.
Jaridar Punch ta ruwaito Kwamashinan Yaɗa Labarai da Tsare-Tsare Eze Chikamnayo yana cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 11:35 na dare.
“A ranar Talata 15 ga watan Fabarairu da misalin ƙarfe 11:35 na dare, wasu ‘ya bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka afka wa ‘yan kasuwa a Sabuwar Kasuwar Shanu ta Omumauzor da ke Ƙaramar Hukumar Ukwa ta Gabas,” in ji shi cikin wata sanarwa.
An kai harin ne kwana ɗaya kafin komawar jagoran ƙungiyar ‘yan tawaye ta Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, gaban kotu don fuskantar tuhuma game da zargin ta’addanci a Abuja babban birnin ƙasar.
Hukumomi a ƙasar na zargin ɓangaren ‘yan bindiga na IPOB mai suna Eastern Security Network (ESN) da kai ire-iren waɗannan hare-hare.