Har yanzu gidajen mai da dama a fadin Najeriya ba sa bayar da mai, lamarin da ya kara jefa ‘yan kasar cikin tsananin rayuwa, ya dakatar da walwalar tafiyar al’amura da dama a kasar.
A Abuja da jihohin Lagos, Rivers, Bayelsa, Kwara, Nasarawa, Niger, Kano, Ogun da sauransu, layikan motoci sun cunkushe ‘yan gidajen man da suka rage suna bayar da man.
Matsalar wahalar man da ta samo asali daga shigowar lalataccen man fetur sati biyu da suka gabata, ya jawo hauhawar farashin man a jihohi da dama, yayin da ‘yan bunburutu ke sheke ayarsu.
A Abuja da wasu sassan jihar Nasarawa misali, ‘yan bunburutu na siyar da lita 10 a kan naira 6,000, inda ya kama naira 600 kowacce lita.
Kudin hawa ababan hawa ya tashi a fadin kasar yayinda kuma kananan ‘yan kasuwa suke fuskantar matsalar karyewa saboda kasa gudanar da kasuwancinsu saboda kasa samun man fetur din.
Haka kuma, masu sana’ar siyar da man fetur din, a ranar Laraba an gano su suna kokarin fara tace lalataccen man tun da kamfanin NNPC ya gaza tacewar.
Kamfanin NNPCn dai a ranar Talata da ta gabata ne ta sanar da cewa tana yin iya bakin kokarinta wajen gyara matsalar, bayan ta baiyana cewa lita biliyan 2.3 za su shigo kasar daga yanzu zuwa karshen watan nan na Fabarairu.
Wannan, in ji NNPC, zai gyara matsalar domin za a samu sama da ma yanda ake bukata a kawanaki 30.