News
IPOB da ESN sunsha alwashin tozarta ni saboda na kai musu farmaki – Abba Kyari

Daga yasir sani abdullahi
“An batan suna daga ‘yan kungiyar IPOB/ESN da suka sha alwashin halaka ni, saboda hare-haren da na kai musu a yankin Kudu maso Gabas,” in ji ‘Super Cop’ din a cikin rahoton.
A cikin wani rahoton da kwamitin ya mika wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, wanda shi kuma aka mika shi ga hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC), Kyari ya ce haramtacciyar kungiyar IPOB da reshenta na tsaro, ESN na bin sa saboda farmakin da aka kai musu a Kudu maso Gabas.
Kyari, wanda bai musanta saba ka’idojin ‘yan sanda na kafafen sada zumunta na rundunar ‘yan sandan Najeriya ba, ya sha kakkausar suka daga kwamitin saboda yadda an taba yin gargadi ga jami’in da ya aikata hakan a baya.