News
YANZU-YANZU: Ganduje ya sake ayyana su Shekarau a matsayin Banza-7

Daga yasir sani abdullahi
Gwamnan Jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sake kiran ‘yan G7 a matsayin Banza 7 a karo na biyu, duk da cewa a baya Gwamnan ya karyata fadin hakan a karon farko.
Ganduje ya bayyana hakane cikin wani sakon bidiyo da yake yawo a kafafen sadarwa biyo bayan watsai da hukuncin tsagin Malam Ibrahim Shekarau, Sanatan Kano ta tsakiya.
A ranar Alhamis ne kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun birnin tarayya ta yanke na soke zaben tsagin Ganduje.
Da take tabbatar da daukaka karar da bangaren jam’iyyar APC na Kano karkashin Gwamna Ganduje ya shigar, kotun daukaka kara ta ce babbar kotun ba ta da hurumin shari’ar tun a farkohukunci
Rashin gamsuwa da hukuncin da babbar kotun ta yanke, kungiyar Ganduje ta garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
Hakazalika, a hukuncin da ta yanke, kotun daukaka kara ta ce lamari ne na cikin gida na jam’iyya mai mulki, don haka ya kamata shugabannin jam’iyyar APC su yanke hukunci.