News
Abdulmumin Kofa na fuskantar kora a FHA sakamakon aikata mummunan laifi

Daga yasir sani abdullahi
Hukumar Kula da Gidaje ta Taraiya, FHA, ta tuhumi Babban Daraktan ta da ke kula da Bincike, Ƙirƙira da Ci gaba, Abdulmumin Jibrin Kofa, sakamakon zargin aikata mummunan laifi.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa tun da fari, Kofa shi ne Babban Darakta mai kula da Ci gaban Kasuwanci (Cinikaiya, Kamfanoni da Gidaje), amma sai mahukuntan hukumar su ka nemi izinin fadar shugaban ƙasa da a rage nasa matsayi bayan ya yi rigima da Manajan Daraktan hukumar, Gbenga Ashafa.
A na zargin Kofa, wanda shi ne, wanda shi ne Darakta-Janar na Ƙungiyar Goyon bayan Tinubu da ƙin amsa takardar tuhuma da Manajan-Daraktan FHA ɗin ya aike ma sa, inda a ke zargin shi da tafka manyan laifuka.
Tuni dai a ka kafa wani kwamiti na ladabtar wa domin bincike zarge-zargen da a ke yi wa Kofa.
Har ma an rubuta wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 15 ga FabrairuFabrairu da sa hannun shugaban kwamitin, Zubairu Salihu, inda a ka baiwa Kofa ɗin umarnin ya gurfana a gaban kwamitin kafin gobe Juma’a ko kuma a kore shi da ga ma’aikatar.
Kawo yanzu dai, ba a samu jin 5a bakin Kofa ɗin ba.