Connect with us

News

Sevilla da Barcelona na takarar sayen Sadiq Umar na Almeria

Published

on

1645080327796
Spread the love

Daga muhmmad muhmmad zahraddin

Kungiyar kwallon kafa ta Sevilla ta fara shirye-shiryen daukar dan wasan gaban Najeriya da Almeria Sadiq Umar.

Yanzu haka kulob din da ke birnin Seville da zaune ne na biyu a teburin gasar La Liga ta Sfaniya.

Advertisement

Sevilla ta ce Sadiq ne sahun gaba cikin yan wasan da ta ke shirin saye da zarar an kammala kakar da ake ciki da dama ta kusa karewa.

Irin yadda ta rike wuta da cin wasanni, akwai yiyuwar Sevilla ta samu zuwa gasar zakarun turai badi, wanda hakan zai bai wa dan wasan damar kara nuna kansa a idon duniya.

  To amma akwai alamun Sevilla ta fuskanci abokan takara a cikin Sfaniyar, don kuwa tun kafin su shiga nemansa rahotanni sun nuna cewa Barcelona tuni ta fara batun kulla ciniki da Almeria don sayen dan wasan.

Advertisement

Sadiq Umar ya tafi Almeria da ke mataki na biyu a Sfaniya da ake kira ‘Segunda division’ daga Partizan Belgrade da ke Serbia a watan Octoban 2020, kuma tun zuwan sa ya zama kashin bayan kungiyar.

A kakar da ta wuce Sadiq mai shekaru 25 ya ci kwallaye 20 a wasanni 38, duk da basu samu zuwa gasar La Liga ba.

Kuma tuni ya ci kwallaye 11 a bana cikin wasanni 24 da ya buga.

Advertisement

Irin wannan bajinta ce kamar yadda jaridar Les Transfert ta ruwaito, ta ja hankalin Sevilla har ta yadda za ta biya kudin kwance yarjejeniyar sa da Almeria don ta kulla wata sabuwa dashi.

Dama Sadiq Umar na da yarjejeniya ne da Almeria daga nan zuwa 2025.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *