News
Yanzu-Yanzu: Mutum 17 sun mutu sanadiyar hatsarin mota.
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Mutane goma sha bakwai sun rasa ransu sanadiyar wani hatsarin mota da ya faru a yau Juma’a
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne a titin Ibadan zuwa Lagos adaidai gadar Isara (Isara Bridge)
Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon taho mu gama da wata motar safa kirar Mazda tayi da tankar mai.
Wasu mutane da dama sun jikkata.