News
Rashin Tsaro: Masari ya yi sabuwar dokar hana dabancin siyasa da manna fastoci a ko ina

Daga yasir sani abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya rattaba hannu a wata sabuwar doka a yunƙurin sa na magance rashin tsaro a jihar.
Yahaya Sirika, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, shi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Katsina.
Sirika ya yi bayanin cewa gwamnan ya yi amfani ne da sashi na 176(2) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 da ya baiwa gwamnan jiha ikon yin doka a kan kansa.
A cewar sa, dokar, wacce ta fara aiki tun 1 ga watan Janairu, ta yamma dukkanin wani nau’i na dabancin siyasa da aikata wasu Laifuka makamantan hakan.
Kwamishinan ya ƙara da cewa dokar ta kuma hana manna fastocin siyasa a rawul-rawul, gine-ginen gwamnati, ofisoshi da sauran guraren jama’a a jihar.
Ya ce dokar ta hana duk wani taro na ƴan baranda siyasa da su ka haɗa da Bacha, Ƙauraye, koma wanne irin suna a ke kiransu, da zai razana al’umma a jihar.
Sirika ya yi gargaɗi cewa duk wanda ya saɓa dokar za a kama da kaifin karya sashe na 114 na dokar ‘penal code’ ta jihar.