News
Buhari yafi matasa da yawa koshin lafiya – Garba Shehu

Daga kabiru basiru fulatan
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa “Shugaba Buharin yafi mafi yawan matasan da suke kalubalantar sa akan matsayin lafiyar sa, koshin lafiya”.
Shehun ya fadi hakan a ranar Alhamis, yayin wata hira da yayi a Channel TV, a tsarin allon gani – gaka na (zoom).
Buhari, yanzu haka ma yana Brussels da Belgium domin halattar taron koli na shida 6 na kungiyar hadaka ta tarayyar Turai da Africa (EU-AU).
” shugaban kasa garau yake. Mu a gurinmu, abin burgewa shine, mutane sun fara jin dadin cewa shugaban kasa yana cikin koshin lafiya, kamar yadda wasu daga hotunan nan suka nuna”. Inji Garba.
” Mun sha fada cewa, shugaban yafi da yawa daga cikin matasan da suke kalubalantar sa akan matsayin lafiyar sa, koshin lafiya. Hakan ko ya bayyana karara daga abin da ya fito daga kasar Belgium”.
Tunda ya kama aiki, shugaba Buharin yake jele zuwa kasar Birtaniya, akan matsayin lafiyar sa ; lamarin da ya janyo Sanya alamomin tambaya akan koshin lafiyar shugaban.
A wani rahoto da jaridar The Cable suka wallafa, a shekarar 2021, an gano cewa Buhari ya shafe kimanin kwanaki dari da saba’in 170 a kasar Birtaniya yana fafutukar lafiyarsa, tun bayan shigar sa Ofis.