Opinion
Babu karancin man fetur a mulkin buhari sai dai ace tsada-Muhammad Muhammad zahraddin

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Idan mukai duba da gwamnatocin da suka gabata duk adaawarmu sai mun sarawa gwamnatin Buhari akan wadatuwar man fetur, saboda haka bai kamata mu zargi gwamnatin Buhari a karancin Man fetur ba, sai dai muce yayi tsada kuma duk tsadarsa kanema ka samuma ai arziƙine.
Idan zamu kalli gwamnatin Buhari da duba na adalci tunda muka zabeshi a 2015, ba’a samu ƙarancin Man fetur ba a fadin kasa baki daya (Nationwide) sai awannan tsakanin.
Saɓanin gwamnatocin da suka shude wadanda ƙarancin man fetur ya zama ruwan dare a mulkinsu musamman a watannin da ake yin wasu bukukuwa ( festivals) din da zai sa a tafi hutu (public holidays).
Amma a mulkin shugaba Buhari ne muka manta da wadancan matsalolin saboda munyi bye bye da matsalolin karancin man fetur.