Opinion
Tarbiyyar ‘ya’yanmu a makarantu
Daga maryam bashir musa
Yana daga babbar matsalar mutum ya sanya yaronsa a makarantar ‘ya’yan elites da pseudo elite da wannabe elites da sauran irin wadannan tarkacen, shi ne ragargajewar tarbiyya. In mutum bai yi wasa ba sai an wayi gari yaronsa ya harbu da guba a zuciyarsa wadda za ta halaka shi har abada.
Na taba kai yarona wata makaranta da nake ganin lallai zai fi samun karatu. Inda Allah Ya taimake ni sai na ji wani malami a makarantar yana ba wa abokinsa labarin yadda kwata-kwata yaran ba su da tarbiyya da kuma irin yadda tunaninsu yake a lalace. Ai babu shiri, kawai sai na dauke yarona na sauya masa da wata.
Ko a makarantun “ya ku bayi” din ma ana samun rashin tarbiyyar amma bambancin shi ne, su malamai suna iya hukunta su, kuma ana iya ladabtar da yaro, sabanin wadancan da su ko tsawa ma mai gigitawa ba a fiye son yi wa yaro ba.
Babban abu mai muhimmanci dai shi ne iyaye su kula da tunanin yaransu, ko ma a wacce irin makarantar suke. Akwai lokacin da yarona ya zo ya ce wani malaminsu wai ya ce musu karatun addini ba shi da muhimmanci. Na ce to me kuka ce masa? Ya ce gabadayan ajin kalubalantar sa suka dinga yi da hujja har sai da ya ajiye wannan maganar. Sai na ce masa duk lokacin da ya sake yin wannan maganar ya fada min. Na yi niyyar kai shi kara gaban hukumar makarantar, kuma public school ce fa!
Yana da muhimmanci iyaye su dinga zama da yaransu suna bibiyar abubuwan da ake koyar da yaransu a makarantun boko da na Islamiyyu, tare da lura da irin abubuwan da ke gudana ta hanyar bibiyar tunanin yaransu. Wannan zai taimaka wajen saitin tunaninsu.
In mutum kuma zai iya to kada ya bar su haka ya saka musu karatu a gida wanda za su dinga yi, yana ba su damar fadin duk fahimtarsu domin saita musu tunani da hujjoji. Wannan zai yi musu turke insha’Allah.
Allah Ya kare mu, Ya kare yaranmu daga gurbatar tunani.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
