News
Gidauniyar Alhaji Falalu Abba ta Kai tallafin ruwa unguwar darerawa dake bachirawa a karamar hukumar Gwale

Daga Abdulkadir Muhammad Sani
Gidauniyar Alhaji Falalu Abba ta Kai tallafin ruwa unguwar darerawa dake bachirawa a karamar hukumar Gwale lamarin da yayi wa al,ummar wannan yanke dadi sosai
inda me magana da yawun kungiyar manniru Abdurrazak Wanda aka fi Sani da matawallen Fagge yace sakamakon yadda yankin ke fama da matsalar ruwa yasa suka ga ya kamata ace sun kai tallafin ta karkashin jagoransu wato Alhaji Falalu Abba.
Shima a nasa jawabin babban limamin yankin Sheik Lawan Sheik Jabir bayyana jindadinsa yayi Kuma kari damasu hannu da shuni dasu danga tallafawa al,umma.
Daga karshe yayi addu,ar samun zaman lafiya kano dama kasa baki daya.