News
Kofar sulhu a bude take tsakaninmu da bangaren Shekarau — Ganduje

Yasir sani abdullahi
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ƙofar sulhu a buɗe take tsakaninsu da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau.
A cikin wata tattauanwa da BBC ta yi da shi, Ganduje, ya ce yanzu lokaci ne na tafiya tare da mayar da hankali kan harkokin ci gaban dimokraɗiyya.
Gwamnan na Kano, ya ce “Muna rokon ‘yan uwanmu a zo a hada a hannu gaba ki daya don a yi wannan tafiya tare, sannan kuma ina so na sanar da ‘yan jam’iyya cewa a dauka damara don yanzu za a shiga gwagwarmayar zabe”.
Ganduje ya ce “Yana da matukar muhimmanci shugabannin jam’iyya su san aikinsu ta yadda za a tafiyar da jam’iyya akan tafarkin dimokradiyya”.
Gwamnan ya ce, idan ana so a shirya ba a duba abubuwan da suka faru a baya, su fatansu azo a zama tsintsiya madaurinki daya.
Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce duk da batun za su daukaka kara zuwa kotun koli wannan daban domin dimokradiyya ce, kuma hakan ba zai hana azo a dai-daita a ci gaba da tafiya tare ba.
Ya ce.” Batun kwamitin da uwar jam’iyya ta nada ni shugabanci na yin sulhu yana nan yana jiransu domin duk mun yi tanadin yadda za a gudanar da dai-daitawar su kawai muke jira”.
Waiwaye
A ranar Alhamis ne dai kotun daukaka kara ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ga Abdullahi Abbas, kuma sa’o’i da yanke wannan hukuncin uwar jam’iyya ta kasa ta mika masa takardar shaidar shugabanci, matakin da bai yi wa ɓangaren Shekarau dadi ba.
Bangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta na jam’iyyar APC a Kano ya ce za su tafi Kotun Koli don ci gaba da kalubalantar bangaren su Gwamna Ganduje a rikicin APC na Kano.
Tsohon gwamnan Kanon ya kuma nuna rashin jin dadinsa da wasu kalmomin batanci da ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da su jim kadan bayan hukuncin kotu da ke cewa bangaren gwamnan ke da halastaccen shugaba.
Kano dai babbar jiha ce da APC ta daɗe tana nanata tasirinta a siyasar Najeriya, abin da yasa APCn ke ƙara ƙoƙari wajen ganin ta hana wannan ɓaraka da ta kunno kai a jihar ƙara tsawo da faɗi.
Idan aka gaggara maslaha tun da wuri babu mamaki wannan rikici ya kassara tasirin da APCn za ta iya yi nan gaba.
Ko da yake ‘ya’yan jami’iyyar na da kwarin-gwiwar sulhu zai tabbatu a tsakaninsu.