News
Ƴan ta’adda sun kashe jami’an ‘Civil Defence’ 4 tare da wasu mutane 6 a Naija

Daga yasir sani abdullahi
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Naija ta ce ƴan ta’adda sun kashe jami’an hukumar tsaro ta ‘Civil Defence’ huɗu a yayin wani hari da su ka kai kan ƙauyen Galkogo da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a jihar.
Kwamishinan Ƴan Sanda a Jihar, Monday Bala Kuryas ne ya tabbatar da harin a tattaunawa ta wayar salula da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a jiya Litinin.
Ya ce ƴan bindigar su ka kashe wasu mutane 6 a harin da su ka kai da sanyin safiya.
Kuryas ya yi bayanin cewa ƴan bindigar sun kutsa kai garin ne a kan babura, inda su ka kona gidaje takwas da kuma wani gini da a ke yi wa kwaskwarima, mallakin rundunar tsaro ta haɗin gwiwa.
Ya ce tuni dai a ka aika rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da sojoji da ƴan sanda da su ka ƙware a salon yaƙi domin bin diddigin ƴan ta’addan.