News
Kotu ta yanke wa kurma hukunci kashi uku sakamakon sayar da wiwi a Kano

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kotun Majistare mai lamba 47, ƙarƙashin Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan, a jiya Litinin ta yanke wa wani kurma hukunci har kashi uku.
Tun da fari dai, an gurfanar da kurman ne bisa tuhumar haɗa kai da uzzurawa al’umma wajen haɗin gwiwa da wasu ɓatagari su na siyar da tabar wiwi.
Ko da jami’in kotun, Auwal Yakubu Abdullahi ya karanto masa tuhumar, nan take ya amsa laifin sa, inda hakan ya sa kotu ta yanke masa wannan hukuncin.
Hukuncin farko, an yanke masa wata 6 ko tarar naira dubu 10, sai kuma ɗaurin shekara 1 ko tarar naira dubu 30, sannan kuma sai ɗaurin wata uku ko tarar naira dubu 10.