Gwamnan jihar Kaduna da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ya koka cewa matsalar hare-haren ‘yan fashin daji na dada kamari a shiyyar kuma kasar ba ta da isassun jami’an tsaron ke iya magance ta.
Kan haka ne ya ce shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na yankin suka yanke shawarar shigowa da na’urorin harba makamai da ake iya sarrafawa daga nesa daga kasar Turkiyya domin taimakawa sojojin saman a kasar wajen murkushe su.
Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a dazu yayin wani taron manema labarai a fadar Shugaban kasar da ke Abuja.