
News
Yadda ƴan Ukraine ke ɓuya a ɗakunan ƙarƙashin ƙasa da aka gina a yaƙin cacar baka

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Mutane sun fara kwarara zuwa ɗakunan ƙarƙashin ƙasa na kariyar harin nukiliya da aka gina a yakin cacar baka.
Ɗakunan na bayar da mafaka ga ɗaruruwan mutane a Ukraine a wannan lokacin da yaƙin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya ƙaddamar ke ƙara ƙamari.

Ɗakunan asali na ma’aikatan wata masanata ne amma an daina amfani da ita da daɗewa.Ɗakunan na ƙarfe ne mai kauri, bangon ginin kuma na da kariya.

Masu agaji sun yi tanadin kayan abinci
A dakunan da ke ƙarƙashin ƙasa an jera gado da dama masu nauyi na ƙarfe, da za su iya ɗaukar mutum 700.