News
Kamfanin BUA ba zai ƙara ko kobo a kan farashin kayansa ba — Diloli
Daga yasir sani abdullahi
Manyan dilolin kayaiyakin kamfanin BUA Group sun tabbatar da cewa kamfanin ya yi alƙawarin ba zai ƙara farashin kayayyakin sa ba har zuwa lokacin azumi da ma bayan nan.
Wani babban dilan kayayyakin BUA, Alhaji Muhammadu Adakawa, yayin gana wa da manema labarai a jiya Litinin, ya baiyana cewa sun gana da Shugaban Kamfanin BUA Group, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu kuma ya tabbatar musu da cewa ba zai ƙara ko kobo a kan kayaiyakin sa na abinci ba.
Ya ce Abdulsamad ya tabbatar musu da cewa ba zai ƙara farashin sukari, taliya, fulawa, siminti da sauran kayaiyakin masarufi ba.
A cewar Adakawa, tuni wasu kamfanunuwa sun ƙara naira 1,500 zuwa naira 1,700 a kan buhun suga, inda ya nuna rashin jin dadi a kan haka kuma ya tabbatar da cewa BUA ba zai ƙara kuɗi ba.
Adakawa ya yi kira ga ƴan sari da su ji tsoron Allah ka da su ƙara farashin kayaiyakin BUA da su ka sara tun da su ma ba a yi musu ƙari ba.
Adakawa ya kuma 5abbatar da cewa BUA zai kawo kaya masu ɗumbin yawa domin kada a samu ƙarancin kaya, musamman ma da azumin watan Ramadan ke daf da zuwa.