News
Matasa na cikin barazanar gamuwa da masatalar ji — WHO

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Hukumar lafiya ta Duniya dai ta ce matasa sama da biliyan ɗaya ne a duniya ke cikin barazanar gamuwa da matsalar ji sosai saboda yawan jin sauti ko hayaniya ba tare da kiyayewa ba.
Dakta Usman Iro Dan Sani, wani ƙwararren likitan kunne a babban Asibitin kunne, hanci da kuma maƙogwaro wato ENT na Kaduna, ya shaida wa BBC yawan kara ko jin kide-kide musamman ga matasan da ke sanya abin jin sauti wato eye piece a kunnesu na da matukar illa ga kunnen.
Ya ce,” Yawan kara da kide-kide ko hayaniya a hankali suke cutar da kunne ba tare da mutum ya sani ba”.
Likitan ya ce sanya ear piece a kunne tamkar sanya babbar lasifika ne a cikin kunne, musamman ma idan ana kure karar da kuma dadewa da shi a kunne kamar yadda matasa ke yi, to lallai da sannu a hankali za su ji suna fuskantar matsalar ji.
Dakta Usman Iro, ya ce,” Abu mai amfani a nan shi ne barin amfani da ear piece din ko kuma a rinka rage karar idan an saya a kunne”.
Likitan ya ce, ga wadanda ke aiki ko sana’a a wuraren da akwai kara ko hayaniya to su rinka daukar hutu su je su zauna a wajen da babu kara.
Ya ce kamar yadda jiki ya ke son hutu, to shima haka kunne ke son hutu don ya ci gaba da ayyukansa.
A cikin wata tattaunawa da BBC ta yi da shi, ya ce kunne abu ne mai matukar muhimmanci sosai, saboda ‘Ji’ shi ne rayuwa
Dakta Usman Iro, ya ce,” Kunne abu ne mai matukar muhimmanci sosai domin ji shi ne rayuwa, ba za a taba hada rayuwar wanda ke ji da wanda baya ji ba”.
Likitan ya ce, daga ji ne ake koyan ilimi, ake sanin abubuwan da ke faruwa na yau da kullum sannan da ji ne ake sauran mu’amala.
Dakta Usman, ya ce akwai hanyoyin da mutum zai bi ya gane kunnuwansa lafiya lau suke, kamar idan ana yi wa mutum magana da karfi sannan ya fahimci abin da ake cewa ko in ciwo a kunnen ko jin wasu kara ba na yau da kullum ba, ko kuma kaikayi ko fitar ruwa da dai sauransu, to wadannan alamomi ne na cewa akwai matsala a kunnen mutum
Kwararran likitan kunnen, ya ce, “Mutane su daina kwakular kunne ko zama a wajen da yake akwai kara mai yawa da hayaniya, mutane su kiyaye da duk wadannan don lafiyar kunnuwansu”.
Ya ce, ga masu dattin kunne, ko mutum bai taba su ba, ma’ana ya goge su ba, da kansu za su fito wajen kunnen wanda har za a iya gogewa.
Amma idan har dattin kunnen ya taru da yawa har ya fara sa mutum ba ya ji sosai, to mafi kyawu shi ne ya je asibiti, in ji likitan kunnen.
Karin bayani
Wadannan bayanai dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin zagayowar ranar ji ta duniya wadda Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta kirkira.
Ana gudanar da bikin ne a duk ranar 3 ga watan Maris na kowace.
An kirkiri ranar ce da nufin wayar da kan jama’a musamman matasa a kan muhimmancin ji da kuma yadda za a kare kunne daga fuskantar duk wata matsala ta ji.
Hukumar Lafiyar ta kiyasta cewa akwai mutum fiye da biliyan daya da miliyan dari biyar da ke fama da matsalar ji a duniya, kusan kaso 20 cikin 100 na al’ummar duniya ke nan.
Taken ranar ta na bana shi ne ‘Idan mutum na son ya tsufa da kunnensa, to ya kiyaye abubuwan da yake ji.