News
Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin man fetur ba: Adesina
Daga yasir sani abdullahi
Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari Mista Femi Adesina , ya bayyana cewa ba mulkin Buhari bane kadai aka fara wahala da tsadar man fetur ba.
Tsawon wata guda yanzu, Najeriya na fuskantar rashi da tsadar man fetur inda mutane ke kwana da motocinsu a gidajen mai.
A jawabin mako-mako da Adesina ya saba, ya bayyana cewa yan Najeriya zasu jure saboda sun jure ire-iren wadannan matsaloli kafin lokacin mulkin Buhari.
“An samu matsalar gurbataccen mai a baya a kasar nan. Mun kwana na tsawon kwanaki da makonni a gidajen mai kuma mun rayu. Wannan ma zamu rayu. Ko ta kaka.”
“Ina kira gareku don tunatar muku da cewa abubuwa basu gurbacewa kasarmu ba.”
“Rashin mai zai so ya tafi. Yan Najeriya kuwa masu godiya zasu ji dadi.”
Kamfanin mai na NNPC ya sha nanatawa cewa, akwai isasshen mai a ƙasar, amma har yanzu mutane suna ci gaba da shan baƙar wahala a gidajen mai, ta hanyar bin dogayen layuka kafin su sha man.