News
Duk dan Najeriya da zai kai dauki Ukraine zai biya dalar Amurka dubu guda.
Daga khadija Ibrahim Muhammad
Dukkanin mayakan sa- kai daga Afirka da ke son taimaka wa Ukraine a yakin da ta ke da Rasha zai biya akalla dala dubu guda na visa da kuma tikitin jirgin gabanin samun damar iya kai dauki.
Jaridar ta PUNCH ta ruwaito ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya na sanar da hakan ga dandazon ‘yan Najeriyar da suka taru a harabarsa da ke Abuja don shiga sahun mayakan sa kai da za su taimaka wa kasar a yaki da Rasha.
Babban sakatare a ofishin jakadancin na Ukraine Mr Bohdan Soltys ya tabbatar da cewa duk dan Najeriyar da ke son shiga yakin dole sai yana da horon Soji haka zalika sai ya biya dala dubu guda dai dai da kusan Nairar Najeriyar dubu 500.
Tuni dai wasu ‘yan Najeriyar suka fara janyewa daga yunkuri kai dauki kasar ta Ukraine a cewar Jaridar saboda yawan kudin da aka bukata kafin kai wannan gudunmawa.
Wata hira da jaridar ta yi da tsohon mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Adedayo Adeoye, yace kamata ya yi a tura masu son zuwa Ukraine din yaƙi jihohin Borno, Yobe da sauran jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya domin yakar ‘yan ta’adda.
Adeoye ya ce shirin da ‘yan Najeriya ke yi na kaiwa kasar Ukraine domin fuskantar Rasha shirin kashe kai ne kuma basu fahimci irin hadarin da hakan ke tattare dashi ba.