Connect with us

News

Zabtare albashin ma’aikata: Ana gab da shiga sabon yajin aiki a Kano

Published

on

FB IMG 1646171999310
Spread the love

mujahid danllami garba

 

 

Advertisement

Kungiyoyin ma’aikata a Kano na gab da shiga yajin aiki biyo bayan hukuncin gwamnatin jihar na komawa ga albashin da daga watan Fabrairu.

Hakazalika, kungiyoyin ma’aikatan sun yi watsi da bukatar gwamnatin na biyan ma’aikatan kananan hukumomi 18,000 da kuma zabtare albashin ma’aikatan jiha, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar Kano, Kabiru Minjibir, wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan wani taron gaggawa a ranar Alhamis, ya ce kungiyar ta yanke shawarar ne bayan gwamnati ta ki yarda da bukatar dawo da kudaden da aka yanke a albashin.

Advertisement

Ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta hannun shugabar ma’aikata, Barista Binta Lawal Ahmed, ta fada ma kungiyar ma’aikatan cewa gwamnati ba za ta iya biyan karancin albashi N30,000 ba saboda raguwar kudaden shiga da ta samu daga gwamnatin tarayya a watan Fabrairu.

A cewar Minjibir, shugabar ma’aikatan ta yi ikirarin cewa jihohi 36 da birnin tarayya sun raba naira biliyan 544 a watan Fabrairu sabanin naira biliyan 699 da aka samu a watan da ya gabata, lamarin da ya shafi biyan albashin.

Minjibir yace ” “Muna nesanta kanmu daga hukuncin gwamnati na zabtare albashin ma’aikata, da kuma mayar da albashin ma’aikatan kananan hukumomi zuwa N18,000.

Advertisement

“Tabbass hakan zai shafi yan fansho ma. Shugabar ma’aikata ta kiramu tana sanar mana da cewa raguwa a kudaden shiga na FAAC, shine yasa ba za su iya biyan karamcin albashi ba.

“Sai dai kuma, dukka kungiyoyin kwadago, NLC, TUC, JNC, JCF, NUP da kuma kungiyar ma’aikatan gwamnati a Kano sun yi taro inda suka ba gwamnati zabi, wadanda suka hada da tabbatar da toshe IGR da yin tanadi daga kudaden shiga don kara albashi, da kuma mayarwa ma’aikata da kudaden da aka cire daga albashinsu da zaran kudaden FAAC ya karu zuwa naira biliyan 700. Amma gwamnati ta amince da duk shawarwarin da aka bayar illa na mayar da kason da aka cire daga albashin ma’aikata.”

Minjibir ya kaddamar da cewar NLC ta kai rahoton lamarin ga hedkwatarta na kasa, yayin da take jiran mataki na gaba.

Advertisement

Ya nuna takaici kan yadda gwamnati ta mayar da tsohon albashin, duk da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, tare da karancin man fetur, wanda ke yin illa ga rayuwar ma’aikata.

Rahotanni dai na cewa ma’aikatan sun koka kan yadda albashin nasu na Febarairu, yake shigo musu a zaftare, saboda watan ya yi nisa har an fice daga cikinsa da karin wasu kwanaki uku zuwa hudu, ga shi wasu sun ciyo bashi sakamakon rashin biyan kudaden kan lokaci don su samu su yi kalaci.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *