Ministan tsaron Birtaniya ya ce toshe BBC a Rasha da mahukuntan ƙasar suka yi ba zai ceci Putin daga jin gaskiya ba.
Ben Wallace ya faɗa wa manema labarai a Denmark cewa ”Wannan matakin na Rasha kuskure ne, ba zai hana faɗa wa Putin gaskiya ba, mataki ne da ya saɓa wa ƴancin ɗan adam”.
A Kwanakin baya ne dai ita ma Birtaniya ta toshe wasu kafofin watsa labaran Rasha a ƙasarta, kamar yadda sauran ƙasashen Turai suka yi.