News
Na rubuta litattafai a kan matsalolin aure saboda lalacewar sa a cikin al’umma — Marubuciya
Daga khadija Ibrahim Muhammad
Aisha Aminu Ahli, wata yar kishin ƙasa wadda take jagorantar wata kungiyar dake tallafawa marayu, ta yi bikin ƙaddamar da wasu littattafai guda 2 domin ba da gudunmawa wajen taimaka wa rayuwar ma’aura, musamman a ƙasar Hausa.
Ta ce ta rubuta littattafan ne duba da yadda aure ya lalace a cikin al’ummar Hausa.
A zantawarta da manema labarai bayan kammala taron ƙaddamar da littattafan a yau jlJuma’aa Kano, Aisha tace ta rubuta littatafan ne sakamakon yadda ta ga ana samun matsaloli da yawa a gidajen ma’aurata, inda hakan ke haifar da mutuwar auren ɗungurumgum.
” Da yake akwai Kungiyar da nake jagoranta don haka Ina Samun korafe-korafe masu tarin yawa daga ma’aurata wannna tasa na fahimci akwai buƙatar na bada tawa gudunmawar wajen magance matsalolin” Inji Aisha Ahli
Aisha tace littafi na farko ta saka masa sunan “Mace-macen aure a Ƙasar Hausa; wa ke da laifi ” wanda ya kunshi abubuwan da su ke jawo matsalolin aure da kuma hanyoyin magance su.
Shi kuma dlɗayan, in ji ta, sunansa ” Sirrin kwanciyar hankali; mijinki a jakarki matar ka a aljihunka” shi kuma yana bayani ne akan rigakafin Matsalolin aure tun kafin a yi auren da Kuma bayan anyi auren.
“Ni kadai na rubuta littatafan ba tare da wani ya tallafa min ba. Sai dai na sami tallafin yan uwana da yan Kwamitin da mahaifina Allah yaji Kansa da Kuma Mijina” Inji Aisha Ahli
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
