News
APC: an kashe mutane hudu har lahira yayin da Ganduje ya rantsar da shugabanni

Daga yasir sani abdullahi
Cikin wani rahoto da Premium Times ta rawaito, ya bayyana yadda mutane hudu suka rasa rayukansu yayin wani rikicin siyasa, a lokacin da gwamnan Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci rantsar da kwamitin jam’iyyar APC a filin wasa na karamar hukumar Rano, harma wasu suka jikkata a ranar Asabar.
Jaridar tace rikicin ya faru ne tsakanin magoya bayan Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Sule Garo, da kuma dan majalisar tarayya na Rano, Kibiya da Bunkure, wadanda dukkansu ake musu fatan gadon buzun gwamna Ganduje a kakar zaben shekarar 2023.