Connect with us

News

Ana yunkurin tsige kakakin majalisar Jihar Kano

Published

on

Spread the love

Daga mujahid danllami garba

 

 

Advertisement

– An ga kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Murtala Sule Garo, yana tara ‘yan majalisar domin aiwatar da tsigewar

Komai bai yi kyau ba a Majalisar Dokokin Jihar Kano, domin kuwa shirin tsige Shugaban Majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari, da Mataimakinsa Zubairu Hamza Massu, ya taso.

Politics Digest ta tattaro cewa shirin yana da nasaba da goyon bayansu ga tsohon kakakin majalisar Kabiru Alhassan Rurum na takarar gwamna.

Advertisement

An ga kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Murtala Sule Garo, yana tara ‘yan majalisar domin aiwatar da tsigewar.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Abdul Madari, mai wakiltar mazabar Warawa, babban mai shari’a, tsohon shugaban masu rinjaye kuma tsohon kakakin majalisar, Abdulaziz Gafasa, suma suna da hannu dumu-dumu a shirin tsigewar bisa umarnin Garo.

Wani dan majalisar dokokin jihar da ya nemi a sakaya sunansa ya kuma tabbatar da shirin tsigewar a ranar Litinin.

Advertisement

“Makircin tsige shi ya zo ne bayan babban taron jam’iyyar All Progressives Congress na Kano ta Kudu da ya gudana a Rano.” Inji shi.

Duka Cidari da Mataimakinsa sun kasance masu biyayya ga Kabiru Rurum lokacin da yake Shugaban Majalisa.

Garo na daya daga cikin manyan makusantan gwamna kuma na kusa da shi. Jama’a da dama na yi masa kallon wanda zai tsaya takarar gwamna saboda irin goyon bayan da yake samu daga uwargidan gwamna Hafsat Ganduje.

Advertisement

A baya-bayan nan dai ana kallon Sanata Barau Jibrin a matsayin wanda ya fi kowa adawa da Garo amma sai ga shi Rurum ya fito daga sansanin gwamnoni. Hakan ya ba shi karfi sabanin Barau da ke cikin bangaren G7 na APC a jihar.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya da Bunkure, Rurum, yana samun gagarumin goyon baya daga ‘yan majalisar jiha a takararsa ta gwamna.

A cewar Jaridar indaranka, A kwanakin baya ne wasu masu ruwa da tsaki daga Kano ta Kudu suka amince da Rurum a matsayin gwamnan jihar Kano, Ado Doguwa, na kakakin majalisar wakilai da kuma Sanata Kawu Sumaila.

Advertisement

An yi ta tayar da jijiyar wuya da mutanen shiyyar suka yi na karbe mulki daga hannun Ganduje.

A cewar masu ruwa da tsaki, shiyyar har yanzu ba ta samar da gwamna ko mataimakinsa ba tun 1993, don haka suka amince da Rurum.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *