News
Farashin mai ya haura dala 140 a kasuwannin duniya
Daga yasir sani abdullahi
Farashin gangan danyan man fetur ya kara tashi a kwasuwannin duniya, inda ya kai kusan dala 140 a kan kowacce ganga, sakamakon mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.
Rahotanni sun ce yau Litinin an sayar da man akan Dala 139 da Centi 13 kowanne ganga wanda shine irin sa na farko tun wanda aka gani a shekarar 2008.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ministan kudin Jamus da na harkokin waje ke gargadi akan daukar duk wani mataki na haramta sayen man Rasha.
A jiya Lahadi, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yace suna duba yiwuwar hana Rasha sayar da man ta a kasuwannin duniya, matakin da Jamus wadda ke shugabancin kungiyar G7 ke cewa bam ai dorewa bane, domin kuwa hakan zai hana su samun wutar lantarki a Jamus.
Kasar Jamus na daya daga cikin kasashen da suka dogara da Rasha wajen samun gas da man fetur, inda take sayen kashi 55 na iskar gas daga wurin ta da kuma kashi 42 na man fetur.
-
News7 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News4 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News4 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi

