News
Jamhuriyar Benin Ta Saki Sunday Igboho, Bayan Tsare Shi Na Watanni
Daga Khadija Ibrahim Muhammad
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki dan dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Ighoho bayan doguwara tsarewa da ya sha, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Hadin kan Yarbawa a kungiyoyin rajin kare hakkin Yarabawa ta Ilana Omo Oodua Worldwide ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Sanarwar wadda mai magana da yawun Ilana Omo Oodua, Mista Maxwell Adeleye, ya fitar, mai taken, ‘Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta Saki Dan rajin kare al’ummar Yarabawa, Sunday Adeyemo Ighoho ga shugaban Yarbawa, Banji Akintoye; Masanin harshen Faransanci, Adeniran’.
Har yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai game da sakin Sunday Igboho da ke tsare a Jamhuriyar Benin tun shekarar 2021.
Idan baku manta ba, an tsare Sunday Igboho ne tun bayan da ya yi kokarin guduwa Turai yayin da gwamnatin Najeriya ta ayyana nemansa ruwa a jallo.