News
Ministan Sadarwa Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami, Ya Kaddamar Da Motar Da Aka Fara Kerawa A Najeriya

Daga mujahid danllami garba
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya yi gwajin motar lantarki wadda kamfanin (Hyundai Kona) suka kera a Najeriya jim kadan bayan ya karbi bakuncin Hukumar Kula da Kera Motoci ta Kasa (NADDC) karkashin jagorancin shugaban hukumar Darakta Janar Jelani Aliyu a ziyarar aiki.
Tawagar NADDC ta kasance a cibiyar sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital dake Abuja don bincika haɗin gwiwa tare da ma’aikatar a fannonin fasahar Dijital da cigaban Abubuwan cikin gida.