News
Boka ya rataye kansa a Benue

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Boka da duniya ta yi masa daurin dema a jihar Benue daga karshe dai ya yanke shawarar kashe kansa ta hanyar rataya, kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.
Bokan, mai kimanin shekara 42 dai ya rataye kan nasa ne a gundumar Mbakuha da ke Karamar Hukumar Ushongo ta jihar ta Binuwai.
Mutumin, wanda aka bayyana sunansa da Terhemen Lorbee dai rahotanni sun ce an shafe kimanin sa’a 24 ana nemansa, kafin daga bisani a gano gawarsa tana reto a jikin wata bishiya a karshen mako.
Shaidu sun ce ko kafin faruwar lamarin, an ga Terhemen ya koma yin wasu bakin al’adu, lamarin da ya sa iyalansa suka fara shiga damuwa.
Ya mutu ya bar mata uku da ’ya’ya hudu a duniya.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin ta wayar salula.