News
Gwamna Sani Bello ya musanta karɓe shugabancin APC

Daga Khadija Ibrahim Muhammad
Gwamnan Jihar Naija, Abubakar Bello ya musanta karɓe shugabancin APC na riƙon ƙwarya, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai su ke raɗe-raɗi.
Bello ya baiyana hakan ne ga manema labarai jim kaɗan bayan ya jagoranci ganawar da kwamitin riƙo na APC ya yi a yau Litinin a Abuja.
A cewar sa, ya gana ne da shugabannin jam’iyar na jiha kuma ya rantsar da wasu sababbin daga cikin su.
Ya ƙara da cewa ya rantsar da shugabannin jam’iya na jihohi kuma sun ɗauki rantsuwar kama aiki, sannan su ka gana a kan babban taron APC mai zuwa a ranar 26 ga watan Maris.
Da a ka tambaye shi ko a matsayin wa ya jagoranci ganawar, sai Bello ya kada baki ya ce “a matsayin shugaban riƙon ƙwarya tunda Shugaba (Buni) ya yi tafiya.”