News
Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan ta’adda 17 a Borno

Daga kabiru basiru fulatan
Rundunar Sojin Ƙasa ta ce dakarun ta na ‘Operation Hadin Kai, OPHK’, sun hallaka ƴan ƙungiyar Boko Haram da ISWAP a Damasak da ke Ƙaramar Hukumar Mobbar a Jihar Borno.
Shugaban Gamaiya ta rundunar ta Hadin Kai da ke Arewa-maso-Gabas, Christopher Musa ne ya baiyana haka a wata tattauna wa da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Litinin a Maiduguri.
Ya ce kuma jajurtattun dakarun sun kuma cafke ƴan ta’adda uku da ran su.
Musa ya ƙara da cewa dakarun sun kuma kwace babura da makamai iri-iri a yayin fafatawar da a ka yi a jiya Lahadi.
Ya ce dakarun ne su ka rufar wa ƴan ta’addan da dama lokacin da su ka kawo hari kan wani sansani na sojoji da ke daura da kofar fita ta Walada da misalin ƙarfe biyu na dare.
Musa ya ƙara da cewa da ga bisani ne ƴan ta’addan su ka haɗu da ƙarfin sojin Nijeriya da su ka riƙa yi musu luguden wuta a fafatawar da a ka yi ta tsawon nawanni.
Sannan ya ƙara da cewa sojojin sama ma sun rusa yan ta’addan inda su ka datse su sannan su ka ragargaje su.