News
YANZU-YANZU: An tunbuke Mai Mala Buni, Gwamnan Neja, Sani-Bello, zai karbi ragamar shugabancin jam’iyyar
Daga Yasir sani abdullahi
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya isa hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa domin karbar mukamin shugaban jam’iyyar na riko CECPC.
Zuwan sa a yanzu yana nuni da kawo karshen shugabancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin shugaban kwamitin.
A baya dai jam’iyyar APC ta bakin Sakataren CECPC, Sanata James Akpan Udohedehe, ta yi watsi da tsige Gwamna Buni a matsayin labarin karya.
Wannan tsigewar na zuwa ne makonni kadan na babban taron jam’iyyar na kasa da aka shirya yi.