News
YANZU-YANZU: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Sakateriyar Jam’iyyar APC Ta Kasa Dake Abuja

Daga kabiru basiru fulatan
Jami’an tsaro sun mamaye sakateriyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake Abuja.
Akwai rahotannin da ke bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tunbuke gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, daga mukamin shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar.
An tattaro cewa, gwamnan jihar Niger, Sani Bello ne zai karba ragamar jam’iyyar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Amma a yayin martani kan rahoton, sakataren kwamitin rikon kwaryan, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce babu batun sauyin shugabanci a jam’iyyar.
“Hankulanmu sun kai zuwa ga wwani rahoto da aka dauka nauyi wanda ke bayyana sauyin shugabanci na kwamitin rikon kwarya da shirya zaben shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).”
“Rahoton babu gaskiya a cikinsa kuma ku yi watsi da shi. Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) jam’iyya ce da ke da dokoki. Ba kowanne kafa bane ke iya sanar da sauyin shugabanni ba a kafafen yada labarai.
A halin yanzu, dukkan hanyoyin da ke kaiwa sakateriyar a Wuse 2 a rufe suke, hakan ya hana ababen hawa kaiwa da kawowa.