News
Kotu ta ki bayar da belin Abba Kyari
Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Babbar kotu tarayya da ke Abuja wadda ke sauraren karar da hukumar NDLEA ta shigar tana tuhumar babban jami’in dan sanda Abba Kyari da wasu mutum shida ta ki amincewa da bukatar da lauyoyinsa suka mika ma ta na a bayar da belinsa.
Sai dai kotun ta ce za ta saurari bukatar a zamanta na gaba.
Lauyan Abba Kyari ya shaida wa manema labarai a gaban kotun cewa kotun ta dage zamanta zuwa ranar Litinin 14 ga watan Maris domin sake duba batun belin.
Amma ya ki cewa komai game da abubuwan da suka wakana cikin kotun, cii har da mika wuyan da wasu mutum biyu cikin mutum shidan da ake tuhuma da aikata laifukan suka yi.
-
Uncategorized6 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News1 day ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
