Connect with us

News

Matasa biyar sun mutu yayin hakar kasa a Kano

Published

on

Spread the love

Daga Khadija Ibrahim Muhammad

 

Wasu matasa biyar sun rasa ransu yayin da suke hakar kasa a wani rami dake kauyen Dan Lami a karamar hukumar Bichi a nan Kano.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun hukumar kashe gobara Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar a Lahadin nan.

Ya ce matasan sun mutu ne a Asabar din da ta gabata bayan da kasa ta rufto musu tare da rufesu wanda hakan yayi sanadiyyar ajalin su.

Advertisement

Matasan da suka rasu sun hada da Alasan Abdulhamid dan shekara 22 da Muhd Sulaiman mai shekaru 35 sai Masa’udu Nasiru dan shekara 25.

Sauran sune Jibrin Musa dan shekara 30 da kuma Jafaru Abdulwahabu shima mai shekaru 30.

Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce tuni suka mika gawarwakin su ga hukumar ‘yan sanda.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *