News
Za’a iya fuskantar matsalar abinci a Nageriya idan yan bindinga suka ci gaba da kai mana hare-hare

Daga muslim yunus abdullahi
Manoman Arewa Sun Koka Kan Hare-Haren Ta’addanci Ba Kade-Bade, Gargadi Kan Karancin Abinci
Wasu manoman arewacin kasar sun koka da yadda ‘yan ta’adda ke ci gaba da kai musu hare-hare, lamarin da ya tilasta musu barin gonakinsu.
A cewarsu, idan har aka dade ana kai hare-haren, za a fuskanci matsalar samar da abinci, kuma matsalar abinci za ta iya addabar kasar nan ba da jimawa ba.
Isa Yakubu da Moshood Tsaku, manoman kauyen Kurgwi da ke karamar hukumar Qua’an-Pan ta Jihar Filato, a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da jaridar PUNCH a ranar Asabar, sun ce zuwa gona a yanzu ya zama tamkar zuwa yaki, domin manoman ba su da tabbas akan tsaron su.
Yakubu ya ce, “Ina tsoron zuwa gonata, don haka na hana matana da yara ƙanana su zuwa Gona saboda matsalar tsaro.
Hakazalika, Tsaku, wanda ya e ya taba tsira daga harin da ‘yan ta’adda suka kai masa a gonarsa, ya ce ya kariya akan harkokin noma.