News
Buhari ya tafi Landan domin duba lafiyarsa

khadija Ibrahim Muhammad
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tashi zuwa birnin Landan a yau Lahadi domin duba lafiyarsa na lokaci-lokaci.
Tun da fari, shugaban ƙasar ya shirya zuwa Landan ɗin ne da ga Nairobi da ke kasar Kenya bayan da ya halarci Taron Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya, UNEP, kamar yadda Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya faɗa a ranar 1 ga watan Maris da ga Nairobi.
Amma kuma sai shugaban ya dawo Abuja a ranar juma’a, kafin yau kuma ya tashi zuwa Landan ɗin, inda Adesina ya ce zai shafe a kalla makonni biyu.