Connect with us

News

Mu ba yin ku ne?: Firaministan Pakistan ya soki Amurka, Burtaniya, Faransa kan rikicin RASHA da UKRAINE

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Firaministan Kasar Pakistan Imran Khan ya soki kasashen yammacin duniya sakamakon neman sanya dole sai kasar sa ta goyi bayansu kan rikicin kasar Rasha da Ukraine.

Mista Imran Khan ya ma tambayi kasashen na yammacin duniya cikin fushi ” Ko mutanen Pakistan ba yin su ne da za su mai da su kamar yara wajen nuna musu yadda za su gudanar da rayuwansu.

“Mu ba ba yin ku ba ne, saboda haka ba ku isa ku ce sai abin da kuke so shi za mu yi ba, wannan lokaci ya wuce”

Advertisement

“To in ma ban da munafunci irin naku ya za ayi ku zira kuna kallon irin cin zarafin da kasar Indiya ke yi wa al’ummar yankin Kashmir, sun mamaye musu kasa sun kashe na kashewa kuna gani ba ku tsawatarwa Indiya ba kuma sai yanzu za ku ce wai mu tausayawa Ukraine” a cewar Firaministan na Pakistan.

Ya kara da cewa kasar Pakistan ba za ta goyi bayan kowa ba tsakanin Ukraine/NATO da kuma Rasha domin ita wajenta kowa nata ne wannan matsayin kasar kenan kuma a haka za ta ci gaba wanzuwa ba canjawa…

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *