Connect with us

News

Manchester City ta lallasa Manchester United a gasar Firimiya

Published

on

1646593334423
Spread the love

 

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin

 

Advertisement

 

 

Manchester City ta lallasa Manchester United a gasar Firimiya

Advertisement

 

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta casa Manchester United a gasar Firimiya ta kasar Ingila da ci 4-1.

Filin wasa na Etihad ne ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Lahadi 06 ga Maris din 2022.

Advertisement

Manchester United da Manchester City dai na hamayya da juna, wanda hakan ya sa fafatawar ta dauki hankalin magoya bayan kungiyoyi biyun.

Dan wasa Kevin De Bruyne ne ya zura kwallaye biyu a minti na (4′) da (27′)

Kana shima dan wasan kasar Algeria Riyard Mahrez ya zura kwallaye biyu a mintuna na (67′) da (90′)

Advertisement

Sai dai dan wasan Manchester United da kasar Ingila Jadon Sancho ya zura kwallo daya a minti na (21′) da jumulla kungiyarsa tayi rashin nasara da ci 4-1.

Kawo yanzu Manchester City na matakin farko da maki 69 a wasanni 28 da ta buga.

Yayinda kungiyar kwallon kafa ta Manchester United take a mataki na biyar da maki 47.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *