News
YAJIN AIKI: GWAMNANTIN TARAYYA TA CE BA TA DA KUƊIN DA ZA TA BIYA BUƘATUN ASUU
Daga mujahid danllami garba
Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da kuɗaɗen da za ta iya biya wa malaman jami’o’i buƙatun da su ke nema.
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya bayyana haka, yayin da aka tattauna da shi a gidan Talabijin na Channels.
A baya dai kungiyar ASUU, ta ce duk da alwashi da alƙawarin da gwamnatin tarayya ta ɗauka bayan masu shiga tsakani har har yau ba ta cika alkawurran da ta yi masu ko ɗaya ba.
Daya daga cikin alƙawurran da har yau aka kasa cika wa kungiyar ASUU dai shi ne, wanda Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a rubuce cewa za ta aiwatar yarjejeniyar da su ka yi kuma ta sa hannu tun cikin shekara ta 2009.
Minista Ngige, ya ce a gaskiya ba su da kuɗin da ASUU ke bukata a yanzu, amma za su bubbuga su nemo domin farfaɗo da jami’o’in da kayan aiki da gine-ginen da ke da buƙatar ingantawa.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
