Sports
Nijeriya 5700 ne za su amfana da shirin aika kuɗi na Red Cross a jihohi 7 na Arewa
Daga yasir sani abdullahi
Hukumar Nigerian Red Cross Society, NRSC ta ce mutane 5700 ne za su amfana da shirin aika kuɗi a jihohi bakwai na Arewa.
Jami’in rage raɗaɗin ibtila’i na hukumar, Antenyi Oloche, shi ya baiyana haka ga Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Makurdi a yau Talata.
A cewar sa, mata masu juna-biyu guda 100 za su amfana da Naira dubu 10 a kowannen su tsawon wata goma, inda guda 700 za su amfana da Naira 30,500 tsawon watanni uku a Benue.
Oloche ya ce da ga cikin mutum 5700 ɗin, za a baiwa 5000 Tallafin ne domin su rike kan su ta hanyoyi daban-daban, inda 700 kuma za su amfana ne a kan abinci mai gina jiki.
Ya ƙara da cewa mutane 800 da ga Jihohin Benue, Nasarawa, Niger, Sokoto, Zamfara da Kebbi za su amfana da shirin aika kuɗin, inda mutane 900 za su amfana da ga Jihar Katsina.
Oloche ya yi bayanin cewa manufar hukumar ita ce rage raɗaɗin matsalolin tattalin a kan mutane masu ƙaramin ƙarfi, da su ka haɗa da waɗanda ibtila’i ya faɗa musu, annoba da kuma rashin tsaro.
Ya ce tsarin da a ka bi shine a tallafa wa mutane masu buƙata ta musamman, talakawa, waɗanda su ka samu matsalar annobar korona da kuma mara sa lafiya da ke kwance a asibiti.