Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Ronaldo, Rashford, Haaland, Paqueta, Martinelli da Nkunku

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Cristiano Ronaldo zai yi kokarin tafiya Paris St-Germain, inda ake ganin dan wasan na Portugl mai shekara 37 zai hade da Lionel Messi, mai shekara 34, idan Manchester United ta kasa samun damar zuwa gasar Zakarun Turai ta gaba. (Football Transfers)
Arsenal, Newcastle da West Ham na daga kungiyoyin da ke sa ran daukar Marcus Rashford bayan da ake ganin dan wasan na Ingila mai shekara 24 na tunani a kan ci gaba da zamansa a Manchester United. (90Min)
Paris St-Germain ma an ce za ta yi kokarin daukar Rashford idan Kylian Mbappe ya tafi Real Madrid. A bazarar da ta gabata PSG ta nemi sayen Rashford amma kuma United ta nuna cewa ba ta da niyyar sayar da shi. (Mail).
Manchester City da Real Madrid su ne kungiyoyi biyu da ke kan gaba wajen zawarcin dan wasan gaban Borussia Dortmund Erling Braut Haaland duk da cewa Bayern Munich da Barcelona na son shi.

ASALIN HOTON,OTHER
Ana sa ran nan da ‘yan makonni ne za a yanke shawara kan makomar dan wasan na Norway mai shekara 21. (Athletic – subscription required)
Mai kungiyar New York Jets, Robert Wood Johnson na shirin gabatar da tayin sayen Chelsea. Ana ganin Johnson ya san kungiyar sosai da kuma gasar Premier, saboda ya zauna a London, a lokacin da yake jakadan Amurka a Birtaniya. (ESPN)
Haka kuma wani kamfanin jarida na Saudi Arabia, (Saudi Media), ya tuntubi kamfanin Amurka, Raine Group wanda ke dillancin kungiyar ta Chelsea, game da sayen kungiyar daga Roman Abramovich. (Goal)
Newcastle ta fara tattaunawa da Real Madrid domin sayen Eden Hazard, mai shekara 31, wanda ake sa ran zai bar kungiyar ta Sifaniya a bazara. (Defensa Central – in Spanish)
Arsenal ta nuna cewa a shirye take ta yi gogayya da Paris St-Germain a zawarcin dan wasan Brazil Lucas Paqueta, daga Lyon. (Calciomercato – in Italian)
Shi kuwa Gabriel Martinelli, ya ce yana son ya ci gaba da zama a Arsenal domin ya ci kofuna, duk da sha’awarsa da Liverpool ke yi. (Liverpool Echo)
Chelsea da Manchester City na cikin kungiyoyin da ke sa ido a kan dan RB Leipzig kuma dan Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 24 ana ganin zai kai farashin kusan fam miliyan 62. (Foot Mercato, via Express)
Wasu ‘yan wasan Manchester United sun dawo daga rakiyar kwarewa da kuma tsarin kociyansu na riko dan Jamus Ralf Rangnick. (MEN)
Juan Mata zai bar Manchester United ba tare da wata yarjejeniya a kansa ba a lokacin bazara, inda kungiyoyin La Liga ke nuna sha’awarsu a kan dan wasan na Sifaniya mai shekara 33. (Athletic – subscription required)
Kungiyoyi da yawa na nuna sha’awarsu a kan dan wasan Middlesbrough dan Ingila Djed Spence, mai shekara 21, wanda ya nuna kwarewarsa a lokacin zaman aro a Nottingham Forest, inda kungiyoyin Premier bakwai wadanda suka hada da Manchester City da Tottenham, da na Sifaniya biyu da kuma na gasar Jamus ta Bundesliga wadanda suka hada da Bayern Munich da RB Leipzig ke sonsa. (Sky Germany via Sport Witness)