News
Ranar mata ta duniya: Google zai tallafa wa mata masu sana’o’i da dala miliyan 1

Daga mujahid danllami garba
A yau Talata ne kamfanin Google ya sanar da bada tallafin dala miliyan 1 domin tallafa wa shirye-shiryen mata masu sana’o’i su bunƙasa kasuwancin su.
Mojolaoluwa Aderemi Makinde, babbar jami’a a Google, yankin Afirka, ta ce tallafin wani ɓangare ne na wasu tsare-tsare da kamfanin ke ƙirkiro wa domin bunƙasa sana’o’in mata.
Makinde ta baiyana hakan ne a wani taro na yanar gizo a wani ɓangare na bikin tunawa da ranar mata ta duniya.
Ta baiyana cewa bincike ya nuna cewa mata ƴan kasuwa su na samun riba kasa a kasuwancin su ƙasa da maza da kashi 34 cikin 100.
Ta ƙara da cewa nata ba su fita samun tallafin kuɗi a kan maza ba, inda ta ce hakan ne ya sanya kamfanin ya ke sanar da kashi-kashi na tallafi ga kafa domin bunƙasa kasuwancin su.